Idan kina son ki iya cake hadadde wanda ko ba ki da oven za ki iya yin shi, to tsaya ki duba yadda na yi wannan melt cake din.
Abubuwan bukata:
1- 1 cup flour
2- 2 eggs
3- 1/2 cup sugar
4- 1 cup oil
5- 1/2 teaspoon baking powder
6- 1/4 teaspoon baking soda
7- 1 teaspoon flavor of choice
8- 2 tablespoons oreos and lotus biscuits for garnishing
9- 2 tablespoons chocolate for garnishing
10- 1/4 cup condensed milk
11- 1/4 cup heavy cream
12- 2 tablespoons nestle cream
13- 1/2 teaspoon salt
14- 2 tablespoons liquid milk
15- 2 tablespoon crushed Oreos
16- 1/2 cup powdered milk
Yadda ake yi
1- Ki fasa kwai a cikin bowl mai kyau, sai ki amfani da handmixer ko kuma whisk ki ta buga shi, ki zuba sugar ki ci gaba da bugawa har sai ya yi haske ya yi kumfa. Daga nan sai ki zuba mai da flavor.

2- Daga nan sai ki ajiye mixer, ki samu silicon spatula da ita za ki amfani. Ki zuba dry ingredients dinki duka. Ki dinga folding a hankali har sai duka sun hade.

3- Sai ki kawo madararki ta ruwa kadan ki zuba ki kara folding amma ba sosai ba.

4- Daga nan sai ki greasing robar da za ki amfani da ita. Shi wannan cake din ko a cup din roba ko robobin yin alale ana iya amfani da su. Ki zuba rabi a cikin robar.

5- Shi kuma ragowar ki zuba 2 tablespoons na oreos biscuits wanda kika nika ya zama gari.

6- Sai ki jera a cikin steamer ki turara na minti sha biyar zuwa ashirin.

7- Kafin ya turara sai ki dawo wurin hada madarar. Ki samu kyakkyawan bowl, ki zuba condensed milk, heavy cream, nestle cream, powdered milk. Ki mixing dinsu sosai

8- Ga cake nan bayan ya turara. Sai ki juye a container mai kyau ki bari ya huce duka.

9- Sai ki tsiyaya wannan cream a cikin piping bag, daga nan ki zuba a kan cake din sannan ki designing yanda kike so. Sannan ki topping ma da abin da kike so.

10- Sai ki saka a cikin fridge ya yi chilling na minti goma zuwa sha biyar. Daga nan sai a yi serving.

Akwai kayan kitchen a Bakandamiya shopping cikin rangwame da rahusa.