Mandula wani nau’i ne na kayan kwalama, wanda ake yin shi da madara. Yana da saukin yi ga wanda ya tsaya ya koya. Ku biyo ni domin ganin yanda ake yi.
Abubuwan bukata
1- 2 cups milk
2- 1/4 cup sugar
3- 1/4 cup water
4- 1 teaspoon flavor
5- Food coloring (pink)
Yadda ake yi:
1- Ki zuba sugar a cikin kyakkyawan pan, sai ki zuba ruwa ki bari su dahu har sai ya dan fara danko.

2- Sai ki zuba flavor sannan ki kawo madarar ki zuba.

3- Sai ki yi ta juyawa da silicon spoon har sai ya kai wannan matakin sannan ki kawo wani bowl ki raba shi biyu.

4- Sai ki kawo pink food colour ki zuba kadan ki hade shi da kyau.

5- sai ki dora a kan rolling board

6- ki murza da hannunki kowanne ya zama dogo daidai kaurin da kike so.

7- sai ki hade su guda biyun ki yi ta jujjuyawa har sai sun manne da junansu. Daga nan sai ki yanka da wuka daidai girman da kike so.

8- Ga shi nan bayan na gama yankawa

9- Sai ki packaging
