Gullisuwa kayan makulashe ce mai matukar dadi wadda ake yi a cikin gida. Tana da saukin yi musamman idan ka yi dace da madara mai kyau. Wasu tana ba su wahalar yi, ko dai ta narke a cikin mai, ko kuma ta kone. Ku biyo ni ku ga yadda nake yin tawa ta yi kyau da armashi.
Abubuwan bukata:
1- 3 cups milk (ku yi amfani da lactorich ko dano).
2- 1/2 cup sugar
3- 1/4 cup water
Yadda ake yi:
1- ki zuba madara a bowl, ki zuba sugar, da ruwa. Amma ruwan ba a lokaci daya za ki zuba shi ba. Kina yi kina karawa har sai kin yi dough wanda ba ya sticking.

2- Sai ki tanadi mai ki shafe hannunki da shi. Sannan ki dinga gutsura kina luliyawa daidai girman da kike so. Amma dai madara tana kumbura, idan kika yi manya sosai zai iya zuwa cikinsa bai soyu ba.

3- Ga shi nan bayan na gama luliyawa

4- Sai ki dora mai a wuta amma kar ki bari sai ya yi zafi sosai. Sannan wutar kadan za ki saka

5- Kada ki motsa, idan kika motsa duk za ta rogaje.

6- sai ki dinga jijjiga non stick frying pan din a hankali yadda zai dinga juya kanshi. Idan kika sanya cokali zai rugurguje a cikin mai

7- Idan ta soyu sai ki tsame wadda ta yi

8- Ki bari a colander mai ya gama tsiyayewa

9- Daga na sai ki packaging
