Akwai hanyoyi da dama da ake yin meatpie. Amma a gare ni wannan hanyar ita ce best, akwai saukin yi sannan akwai dadi.
Abubuwan bukata:
1- 4 cups flour
2- 250g butter
3- 1 egg
4- 1 tablespoon sugar
5- 1 teaspoon baking powder
6- 1/2 teaspoon salt
7- 1/2 cup chill milk or water
For the filling
1- 1/2 kg minced beef
2- 1 onion
3- 1 spoonful pepper mix
4- Seasoning and spices to taste
5- Curry powder
6- 2 Irish potatoes
7- 2 carrots
8- 1 green bell pepper
yadda ake yi:
1- Za ki fara da hada filling. Ki zuba nama, seasoning and spices, ki motsa har sai naman ya fara canja kala. Sannan ki zuba pepper mix da curry ki motsa. Sai dankali, karas, da koren tattasai ki motsa sannan ki bari su sulala na minti goma.

2- idan za ki hada dough, ki zuba flour a cikin bowl, sugar, gishiri, baking powder, egg, da margarine. Ki motsa har sai ya zama kamar breadcrumbs. Sai ki zuba madara ki karasa motsawa

3- Ki hada soft dough. Sai ki rufe shi ki saka a fridge na tsawon minti talatin.

4- Bayan minti talatin sai ki ciro shi daga fridge, ki flattening ba da tudu sosai ba kuma ba flat sosai ba. Sai ki dora a kan meatpie cutter (za ku samu a Bakandamiya shopping). Ki zuba filling din sannan ki rufe a hankali. Daga nan sai ki ciro shi.

5- Ki hada egg whites da madara ki motsa. Sai ki jera meatpie dinki a kan oven tray sannan ki shafe shi da wannan hadin da kika yi na madara da kwai.

6- Daga nan ki dauka ki saka a pre heated oven ki gasa da wutar sama da kasa na tsawon minti talatin zuwa arba’in, ko kuma idan ya zama golden brown.
