Uwargida! Amarya! Ga yadda ake wani kayan armashi, Fish and boiled eggs sauce, girki ne mai sauki sai dan karen dadi. Ku biyo ni, ku sha labari. To bisimillah!
Abubuwan hadawa
- Kifi (dafaffe)
- Kwai (dafaffe)
- Tumatir (ki yanka)
- Tarugu (ki jajjaga)
- Tattasai (ki yanka)
- Koren wake (ki yanka)
- Karas (ki yanka)
- Lawashi (ki yanka)
- Marasar gwangwani (ba dole bane)
- Kayan kamshi
- Maggi
- Mai
- Albasa
- Gishiri kadan
Yadda ake hadawa
- Da farko za ki dauko dafaffen kifinki ki cire iya zallar tsoka ki raba shi da kaya sai ki ajiye a gefe.
- Dauko dafaffen kwai shima ki yanka shi dan dai dai (karki yanka shi kanana sosai).
- Sai ki daura kasko ko tukunyarki akan wuta ki zuba mai ki yanka albasa ki soya sama sama sannan ki kawo tarugu da tattasai ki sa ki juya suma ki soya sama sama.
- Sannan ki kawo kayan kamshi, da maggi, da gishiri (iya dandanon da zai mi ki) ki sa ki juya, kawo tumatir ki sa ki juya a hankali sai ki rufe nadan wani lokaci kadan.
- Sai ki kawo kifi da kwanki ki zuba a ciki, ki juya sai ki rufe ki rage wuta sosai nadan wani lokaci kadan.
- Daga Karshe ki kawo su lawashi, da koren wake, da karas da masarar gwangwani ki zuba ki juya a hankali sai ki bari sudan turara kadan ki sauke. A na iya cin wannan sauce tare da shinkafa, ko taliya, ko soyayyen doya ko dankali da dai sauransu.
Sannan za a iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake fried rice mai kaza da yadda ake tsiren kaza da sauransu.