Skip to content

Yadda ake tsiren kaza

Share |
yadda ake tsiren kaza
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Uwargida ga yadda ake tsiren kaza cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi tara da kuma steps biyar.

Abubuwan hadawa

  1. Tsokar kaza danye
  2. Yajin borkono
  3. Kayan kamshi
  4. Maggi chicken
  5. Albasa
  6. Tumatur
  7. Karas
  8. BBQ machine
  9. Skewers

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauki yajin barkono ki ki sa a turmi ki kawo kayan kamshi da maggi iya dandanon da zai miki ki sa ki kawo daddawa kadan ki sa gishiri kadan ki sa ki daka ya daku sosai ajiye a gefe.
  2. Dauko tsokar kazar ki ki gyara ki yanka su sannan ki fadada yankan (yankan kamar yanda ake yanka na masu tsire) ajiye a gefe.
  3. Dauko kwano daban ki sa tsokar kazan ki sa ki kawo yajin ki ki bada a kai dauko albaa ki sa ki kara maggi iya dandanon da zai miki sai ki juya komai ya hade da juna sai ki rufe ki sa a fridge nadan wani lokaci ko ki barshi ya kwana a ciki idan da dare ki ka hada shi.
  4. Sai ki dauko hadin kazan ki sannnan ki kawo tsinken tsire ki dauko ki na sokawa a jikin tsinken ki na ajiyewa a gefe Ki kunna BBQ machine na ki idan ya yi zafi ki kawo hadin naman ki ki jera a kai kidan bar shi na dan wani lokaci sai ki juya. Haka za ki yi ta yi har sai ya gasu ki na iya yaryada man gyada da maggi mai ruwa idan ki na cikin gasawa dan ya kara dandano.
  5. Daga karshe, da zarar kinga ya gasu sai ki sauke sannan ki yanka tumatur, albasa da karas a kai.

Karin bayani 

Idan ki na so gashin naman ki ya dan yi yaji za ki iya idan ya yi rabin gasuwa sai ki sauke ki zuba yajin barkono ki a faranti ki sake bade naman da shi, sai ki sake mayarwa akai ki karasa gasawa. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

Average: 3.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading