Skip to content

Egg and vegetable pocket

Share |
egg and vegetable pocket
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Uwargida ki koyi yadda ake egg and vegetable pocket. Wannan egg and vegetable pocket yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi biyu (flour 2cups)
  2. Baking powder 1½tsp (karamin cokali)
  3. Butter cokali 2 (2tbspn)
  4. Nama (dafaffe)
  5. Kwai guda 2
  6. Kayan qamshi
  7. Tarugu(ki jajjaga)
  8. Maggi da gishiri
  9. Albasa (ki yanka)
  10. Kabeji( ki yanka)
  11. Karas ( ki yanka)
  12. Koren wake (ki yanka)
  13. Ruwa ¾ kofi (¾ cup)

Yadda ake hadawa

  1. Da farko sai ki dauko filawa ki tankade ki zuba baking powder da gishiri kadan, ki kawo butter cokali biyu ki sa, sai ki juya har sai ta hade jikinta sai ki zuba ruwa ki kwabata har sai ta hade jiki ta, sai ki rufe ta ki ajiye a gefe.
  2. Ki Dauko naman ki ki sa a turmi ki daka sannan ki kwashe ki ajiye a gefe.
  3. Dauko tukunya ki sa butter ko man gyada kadan, sai ki yanka albasa ki soya sama sama sannan ki kawo tarugu ki sa ki juya.
  4. Sai ki dan zuba ruwa kadan sannan ki kawo nama (wanda kika daka) ki sa ki juya.
  5. Sannan ki sa maggi da gishiri (iya dandanon da zai miki), ki sa kayan kamshi, sai ki juya ki rufe na dan wani lokaci.
  6. Daga karshe ki kawo su kabeji, karas, da koren wake ki zuba ki rufe su dan turaru, sai ki sauke ki ajiye a gefe.
  7. Dauko kwai ki fasa ki yanka albasa kisa gishiri kadan ki buga shi sai ki daura kasko ki dan zuba mai kadan, idan ya yi zafi sai ki zuba kwanki a ciki ki soya (kamar yanda ake suyan kwai) sannan ki ajiye a gefe.
  8. A wannan lokaci sai ki dauko hadin filawarki ki samu waje mai fadi kina yankawa kina murzata da abun murji (rolling) har sai ta yi fadi (kar ki yi ta da kauri kuma ba fale-fale ba yanda zai yage da wuri). Sannan sai ki samu abu round ki fidda shape din cikin sauki.
  9. Dauko kwanki sai ki yanka dan daidai ki fara sawa, sannan ki kawo hadin naman ki ki daura kan kwan.
  10. Sai ki shafa ruwa a gefe daya ki dauko gefe da gefen ki manne shi ki sake dauko dayan gefen ki manne shi shima. Haka za ki yi har sai kin gama.
  11. Ki daura man gyada akan wuta sai ki soya (amma kar ki sa wuta sosai ba), haka za ki yi har sai kin gama.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×