Ku koyi yadda ake dafaffiyar doya da miyar kwai. Wannan hadin na da dadi da kuma sauki wajen hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya.
Abubuwan hadawa
- Doya (gwargwadon bukata)
- Kwai 4
- Albasa 2
- Maggi 4
- Attarugu 3
- Kori
- Man girki
- Tafarnuwa 2
- Gishiri
Yanda akehadawa
- Da farko zaki fere doyarki ki wanke ki sa atukunya da dan gishiri
- Idan yayi sai ki sauke ki zuba a kwanonki
- Ki fasa kwanki ki jajjaga attarugu ki yanka albasarki
- Ki sa kaskonki a wuta kisa mai ya danyi zafi sai ki zuba kwai kisa attarugu, da albasa, da maggi, da tafarnuwa, da kori,
- Sai ki dinga juyawa kadan-kadan kar kisa wuta sosai
- Idaan yayi sai ki sauke ki kawo doyarki ki zuba
Kai jama’a! Wallahi har miyau na ya tsinke. Hmmm