Croissant ya samo asali ne daga Faransa. Wani snack dinsu ne wanda suk mayar da shi na al’adarsu, tamkar dai a ce gurasa ga Bakano. Yana da dadi sosai.
Ingredients
1- 2 cups flour
2- 1 egg
3- 1 tablespoon yeast
4- 1/2 teaspoon salt
5- 2 tablespoons sugar
6- 1/4 cup vegetable oil
7- 125g butter
8- 1/2 cup liquid milk
Yadda ake yi:
1- Ga jerin abubuwan da muke da bukata

2- ki zuba madararki a cikin bowl, sai ki zuba elyeast, egg, oil, flour, salt.

3- Ki hada soft dough. Bayan nan sai ki rufe shi ki bari ya tashi na akalla minti talatin

4- Ga shi nan bayan ya tashi

5- Sai ki raba shi gida takwas. Sannan ki yi moulding din kowanne

6- sannan ki yi flattening. Ki dora a kan tray ki shafe shi da butter. Ki sake flattening wani ki dora a kan wancan shi ma ki shafe da butter. Haka za ki yi har sai kin yi duka guda takwas din. Ana so duka su zama equal sizes

7- Daga nan sai ki rufe shi ki kai a fridge ya yi minti arba’in zuwa awa daya

8- Ga shi nan bayan kimanin awa daya

9- Sai ki barbade shi da flour ki dora a kan working surface ki yi flattening dinsa da fadi sosai

10- Sai ki yanka shi kamar haka

11- Sannan ki nannada shi. Ki ba shi minti talatin har sai ya zama double size dinsa

12- Ga shi nan ya tashi. Sai ki shafa kwai a sama saboda ya yi golden brown din da ake so.

13- Sai ki sa a oven ki gasa na minti talatin.
Za ku samu nau’uka na kayan kitchen kayatattu a shafin Bakandamiya shopping.