Couscous daya ne daga cikin nau’ukan pasta, wanda ake yin shi da semolina flour. Couscous yana daya daga cikin abinci masu saukin sarrafawa, a cikin takaitaccen lokaci za a sarrafa kuma a ci. Haka zalika miyar albasa, tana da saukin yi, sannan tana da kamshi mai dadi wanda ba kowa ne ya san da wannan sirrin ba. A yau na zo maku da yadda za ku sarrafa couscous ya yi wara-wara, sabanin wasu da yake yin kamar tuwo duk ya cabe idan suka sarrafa shi. Ina sabbin Amaren mu da couscous ke yawan bawa kunya, ku shirya tsaf dan ganin yadda ake wannan couscous din daki-daki.
Abubuwan bukata
For the couscous:
3 cups couscous
3 cups boiling water
1/2 teaspoon salt
1/2 teaspoon curry powder
2 tablespoons vegetable oil
For the Sauce:
4 pieces big onions
1 cup of pepper mix (tarugu da tattasai)
4 maggi cubes
1/2 teaspoon curry
1/2 cup vegetable oil
10 pieces cooked meat
1/2 teaspoon black pepper
Yadda ake yi
1- ki dora ruwan zafi a wuta.

2- Ki auna couscous 3 cups (ki yi amfani da measuring cup)
3- Ki zuba vegetable oil, gishiri, da curry

4- Idan ruwan ya tafasa sai ki zuba 3 cups a ciki (Ana zuba ruwa daidai da yawan couscous. Idan kuma ba mai shan ruwa sosai ba ne sai ki rage).

5- Daga nan sai ki rufe ki bar shi ya turara na tsawon minti sha biyar.
6- Ga shi nan bayan ya turara

Yadda ake yin sauce din kuma
1- ki zuba mai a tukunya sai ki saka dafaffen nama ki soya.

2- Idan ya soyu sai ki kawo pepper mix ki zuba a ciki

3- Ki zuba maggi, curry, da black pepper

4- ki gyara albasa ki wanke sannan ki zuba a cikin food processor (idan ba ki da ita ki gurza a grater kamar yadda ake gurza carrots ko kwakwa.)

5- Sai ki juye albasar a cikin sauce din sai ki zuba ruwa kadan.

6- Bayan minti goma zuwa sha biyar sai ki dandana idan komai ya ji sai ki sauke.
7- Ba dole sai da couscous ake serving ba. Za a iya ci da shinkafa, spaghetti, yam da sauransu. Ni dai na ci da couscous.

Muna da food processor, measuring cups, da wasu da yawa daga nau’ukan kayan kitchen a dandalinmu na Bakandamiya Shopping.