Cookies wani nau’i ne na snacks wanda ake yi da flour za a iya cin shi da lemo ko da shayi, sannan za a iya ci haka nan domin kwalama. Akwai hanyoyin da ake yin shi, a yau na kawo muku yanda ake yin piped cookies.
Abubuwan bukata:
1- 2 and 1/2 cups flour
2- 1 cup sugar
3- 1/2 cup butter
4- 1 egg
5- 1 teaspoon flavor
Yadda ake yi:
1- ki zuba butter a bowl, sai ki saka sugar, egg, da flavor ki yi mixing sosai. Daga nan sai ki zuba flour.

2- sai ki mixing. Ana son kwabin kada ya yi tauri sosai kuma kada ya yi ruwa. Daidai yanda za ki iya piping dinsa dai.

3- Ki shimfida parchment paper a saman baking tray. Then ki zuba kwabin a cikin piping bag da babban nozzle ko kuma wanda kike da shi.

4- Sai ki piping dinsa yadda kike so. daga nan ki saka a cikin oven ki gasa na minti sha biyar zuwa ashirin da medium heat.

5- bayan ya gasu na jera a kan cooling rack ya gama hucewa.

6- Sannan na yi packaging
