Akwai hanyoyi da dama na sarrafa tuwon madara. A yau na kawo mana wata hanya mai sauki mai dadi. A ido dai kamar meatpie, nan kuwa zallar madara ce da cakuleti.
Abubuwan bukata:
2 cups milk
1/3 cup sugar syrup (a dafa sugar da ruwa da flavor)
250g chocolate
Yadda ake yi:
1- ki dinga zuba sugar syrup din da kadan da kadan har sai kin hada soft dough na madarar.

2- Sai ki dibi kadan ki flattening dinsa da fadi daidai yadda kike son shi dai. Sai ki dora a kan meatpie curter dinki bayan kin shimfida mata leda.

3- Sai ki zuba melted chocolate a ciki amma ba da yawa sosai yadda za ta zube ba. Sai ki pressing a hankali yadda ba zai bude ba.

4- Haka za ki yi wa sauran duka har sai kin gama.

Ku duba Bakandamiya shopping domin sayayyar kayatattun kayan kitchen.