Cake wani nau’i ne na snacks. Akwai hanyoyi da yawa na sarrafa shi. A yau zan gwada maku yadda na yi cake har kala hudu, da kwabi daya. Na yi amfani da different toasters daga Bakandamiya Shopping.
Abubuwan bukata:
1- 3 cups flour
2- 3 eggs
3- 1 cup sugar
4- 1/2 sachet butter
5- 1/4 cup vegetable oil
6- 1 tablespoon flavor
7- 1 tablespoon baking powder
8- 1 cup milk (liquid)
Yadda ake Yi
1- ki zuba sugar a cikin mixing bowl mai girma. Ki zuba butter da oil

2- Sai ki mixing. Na yi amfani da muciya za ki iya yi da handmixer ko standing mixer idan kina da ita.

3- Ki zuba egg da flavor of your choice

4- Sai ki sa flour da baking powder ki mixing. Daga nan sai ki zuba madara.

5- Sai ki mixing da kyau. Ga yanda kwabin zai kasance.

6- Sai na samu muffin liners/ cupcake liners na zuba batter half na liner din. Daga nan na saka a pre heated oven na gasa na minti ashirin da wutar kasa, daga nan na kunna wutar sama ya gasu na minti biyar.


7- Wannan kuma ga yadda toaster din take nan. Sai da na yi greasing dinta sannan na zuba kwabin a ciki shi ma na gasa na minti goma.


8- Again na yi greasing wannan toaster din. Sai na zuba kwabin a ciki shi ma na gasa.


9- Wannan ma na yi greasing na gasa na minti goma.


10- Ga shi nan duk na jera su bayan na gasa.
