Skip to content

Alalen wake da doya

Share |
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Kin taba jin alalen wake da doya? Idan baki taba ba, yau gashi mun kawo miki uwargida. Nemi wuri zauna ga step by step na yadda za ki yi.

Abubuwan hadawa

 1. Wake
 2. Doya
 3. Attarugu
 4. Albasa
 5. Maggi
 6. Kori (Curry)
 7. Tafarnuwa
 8. Kwai
 9. Gishiri

Yadda ake hadawa

 1. Da farko zaki wanke wakenki ya fita tas
 2. Sai ki fere doyarki ki yanka kanana sai ki zuba akan wakenki
 3. Sannan ki sa attarugu da albasa da tafarnuwa sai a kai miki markade
 4. Idan markadenki ya dawo sai ki zuba ruwan dumi da maggi, da gishiri, dakori, da manja, kuma dama (juya) daidan kaurin alalan
 5. Dama kin dafa kwanki ya na gefe. Sai ki rika daura kullunki a a laida ki na jefa kwan a ciki
 6. Idan kin gama daurawa, sai ki zuba a tukunya ki zuba ruwa ki dora a wuta ya samu kamar minti 45
 7. Da zaran ya dahu za ki ji gida ya dau kamshi. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Alalen wake da doya”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading