Ku koyi yadda ake buns cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi takwas da kuma steps uku.
Abubuwan hadawa
- Filawa kofi 4
- Baking powder cokali karami 4 (tspn)
- Butter cokali babba 4 (tbsp)
- Sugar 1/2 kofi
- Gishiri kadan
- Madara 3/4 kofi
- Nutmeg cokali 2 (tsp)
- Ruwa 1 kofi (250ml)
Yadda ake hadawa
- Ki tankade filawarki a kwano mai dan girma, sai ki zuba baking powder, nutmeg, madarar gari, gishiri sai ki juya.
- Dauko butter ki sa a cikin filawa ki murja har sai ya hade jikansa sai ki sa sugar, ki fasa kwanki a ciki da ruwa ki kwaba shi ya kwabu sosai sai ki ajiye a gefe na dan wani lokacin kamar minti 15-20.
- Daura man gyada a kan wuta idan ya yi zafi sai ki dauko kwabin filawa ki na kamar mulmula shi ki na soyawa a mai har sai ya soyu (kar ki cika masa wuta don kar ya miki tuwo a ciki) sai ki tsane a matsani. A ci dadi lafiya.
Very straightforward !love it!