Skip to content

Yaddda ake buns

Share |
Yaddda ake buns
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake buns cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi takwas da kuma steps uku.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi 4
  2. Baking powder cokali karami 4 (tspn)
  3. Butter cokali babba 4 (tbsp)
  4. Sugar 1/2 kofi
  5. Gishiri kadan
  6. Madara 3/4 kofi
  7. Nutmeg cokali 2 (tsp)
  8. Ruwa 1 kofi (250ml)

Yadda ake hadawa

  1. Ki tankade filawarki a kwano mai dan girma, sai ki zuba baking powder, nutmeg, madarar gari, gishiri sai ki juya.
  2. Dauko butter ki sa a cikin filawa ki murja har sai ya hade jikansa sai ki sa sugar, ki fasa kwanki a ciki da ruwa ki kwaba shi ya kwabu sosai sai ki ajiye a gefe na dan wani lokacin kamar minti 15-20.
  3. Daura man gyada a kan wuta idan ya yi zafi sai ki dauko kwabin filawa ki na kamar mulmula shi ki na soyawa a mai har sai ya soyu (kar ki cika masa wuta don kar ya miki tuwo a ciki) sai ki tsane a matsani. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yaddda ake buns”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×