Uwargida ga yadda ake zigzag potato cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi hudu da kuma steps biyu.
Abubuwan hadawa
- Dankalin turawa
- Wuka mai zigzag
- Gishiri
- Man gyada
Yadda ake hadawa
- Ki dauko dankalin turawa ki fere shi sai ki wanke shi tas. Ki dauko wukanki mai zigzag ki yanka shi kamar yanda ki ke yankan dankali na suya ko kuma za ki iya yanka shi irin yankan da ki ke so.
- Sai ki sake wankewa ki barbada mishi gishiri kadan ki daura man gyadan ki a kan wuta idan ya yi zafi sai ki soya.
Karin bayani
Ita wannan wuka ana iya samun ta a cikin set na abun juice (pro-v).