Yau abin da na zo maku da shi shi ne yadda ake yogo fura. Ba wai fura irin wadda ake dafawa a kirb’a sannan a luliya ba. Wannan dambun fura ne da ake yi cikin hanya mai sauki. Idan kika bi yadda na yi har business za ki iya farawa da shi kuma ya samu karbuwa da yardar Allah.
Abubuwan bukata:
1- 2.5 liters yoghurt
2- 1 and 1/2 cups condensed milk
3- 1 cup powdered milk
4- 1 cup sugar
5- 1/2 cup raisins
6- 1 and 1/2 cups grated coconut
7- 2 cups garin kunu (na gero)
8- 1 cup water
9- 1 tin evaporated milk
10- 1 tablespoon flavor of your choice
Yadda ake yi:
1- Ki zuba garin kunu a babban bowl sai ki dinga yayyafa ruwa ki kwaba shi amma da tauri.

2- Then ki samu hand grater ki dinga murza shi a hankali. A cikin colander mai kyau da tsafta.

3- ki dora colander din a kan tukunya wadda kika zuba ma ruwa. Ko kuma ki yi amfani da steamer ki turara shi.

4- Ki zuba yoghurt a babban roba ki buga shi sosai ko ki saka mixer ki yi mixing dinsa na minti biyu. Sai ki zuba sugar, madarar ruwa, condensed milk, raisins, da kuma madarar gari.

5- Sai ki kawo wannan dambun furar da kika turara ki zuba a ciki.

6- Ki zuba kwakwa wadda kika gurza kanana.

7- Ki saka flavor of your choice. Ni dai na yi amfani da vanilla.

8- Ki saka muciya ki yi ta motsawa har sai komai ya hade.

9- Shi ke nan kin gama. sai ki dura a cikin botteles ko robobin da kike so.

10- Kamar yadda na fada maku za ku iya yin business da shi. To kun ga yadda nake yin packing nawa na sayarwa.

Za ku samu kayan kitchen masu rangwame da rahusa a Bakandamiya Shopping. Kina da bukatar sabunta kayan kitchen saboda wata mai alfarma na Ramadhana.