Wasu na kiran shi tofi, wasu iloka, a wani yanki na Katsina kuma suna kiran shi babandudu. Kayan kwalama ne mai matukar dadi, wanda duk ya iya shan shi, to ba lallai ba ne ya so alewar kasuwa. Yana da saukin yi.
Abubuwan bukata:
1- 1/2 tin condensed milk
2- 1/2 sachet butter
Yadda ake yi:
1- Ki juye madarar a cikin non stick frying pan ko kuma pots. (Amfani da non stick ya fi sauki ga mai yin iloka. Idan ba ku da ita ku duba shafin Bakandamiya Shopping za ku samu original non stick pots da pans).

2- Sai ku zuba butter. Ana iya amfani da mai amma dai na butter ya fi dadi.

3- Sai ki kunna wuta.

4- Ki ci gaba da juyawa a hankali da silicon spatula.

5- Za ki ga ya fara kumfa madarar tana tsinkewa. To daga nan za ki rage karfin wuta don kada ya kone.

6- Idan ya kai wannan matakin kada ki jinkirta motsawa. Ki yi ta jujjuya shi a hankali don babu wuya zai kama.

7- Idan ya yi haka alamun ya gama yi ke nan. Sai ki kashe wuta.

8- Ki juye a kan parchment paper

9- ki tabe shi ya baje da kyau ko kuma dai yadda kike son shi.

10- sai ki sa wuka ki yanka shi ta tsaye amma kada ki bari ya huce duka. Idan ya yi karfi ba zai yanku ba.

11- Sai ki sa almakashi ki yanka shi daidai girman da kike so.

12- Sai ki bar shi ya gama hucewa.

13- Ga shi nan bayan na gama.


14- Nan kuma na yi packaging dinshi yadda nake so. Har business za ki iya farawa da wannan.
