Ga wani salo da za ku sarrafa shinkafa ta yi dadi da kyau mai hana jin yunwa.
Abubuwan buƙata:
1- Shinkafa kofi biyu (Na yi amfani da basmati. Za ki iya amfani da kowacce)
2- Mai rabin kofi
3- Ɗanɗano yadda zai ji
4- Kayan ƙamshi wanda kike so
5- Niƙaƙƙen nama kofi ɗaya
6- Attarugu guda biyar (ko kuma yadda ake son yaji)
7- Albasa guda ɗaya
8- Dark soy sauce (Ba dole ba ne)
9- Gishiri yadda zai ji.
Yadda ake yi:
1- Ki zuba mai a cikin tukunya sai ki zuba albasa da kayan ƙamshi. (Akwai kyawawan tukane a dandalin saye da sayarwa na Bakandamiya kamar dai yadda kuka ga wannan tawa)

2- idan ya yi zafi sai ki zuba Niƙaƙƙen nama, ki saka curry, all purpose spice, da kuma dark soy sauce.

3- sai ki zuba gishiri yadda zai kama naman, ko kuma yadda kike son ɗanɗanonsa. Daga nan ki motsa (ki duba bakandamiya shopping akwai cokulan motsa abinci kala-kala a kan farashi mai sauki).

4- Daga nan sai ki wanke basmati ko kuma shinkafar da kike da ita, ki tsane ta sannan ki juye a kan namanki wanda ya ɗauko dahuwa. Sai ki zuba jajjagaggen tarugu da albasa, ki zuba ɗanɗano.

5- sai ki kara gishiri kaɗan saboda ya shigi shinkafar, ki zuba ruwa makimanci ki sake motsawa.

6- Sai ki rufe ki bari ta dahu (ku duba murfin tukunyar nan kamar wani kyakkyawan kwanon cin abinci. Za ku samu irinta ko ma wadda ta fi ta a Bakandamiya shopping).

7- To ga shinkafarmu nan bayan ta dahu. wannan niƙaƙƙen naman da ya watsu a cikin shinkafar shi ya sa ake kiran ta da ‘Dirty Rice’ tana da daɗi sosai sannan tana da ban sha’awa.

Za ku samu kyawawan plates da sauran nau’ukan kwanonin cin abinci da cokula a Bakandamiya Shopping
