Awara na daya daga cikin abinciccikan da malam Bahaushe ya yi aro daga mutanen China. Inda suke kiran shi da ‘Tofu’ akwai hanyoyi da dama da ake yin ta. Ku biyo ni domin ganin yadda nake yin tawa.
Abubuwan bukata:
1- 2 mudu waken soya
2- 2 liters ruwan tsami
3- 1 cup manja
Yadda ake yi:
1- ki gyara waken soya ki kai a markada. Daga an markada kada ki jira komai, ki zuba manja a ciki. (Amfanin zuba manjan yana hana shi yin kumfa).

2- Sai ki motse shi manja ya kai ko’ina.

3- Ki samu mataci mai tsafta ki tace shi da ruwa makimanci.

4- Sai ki juye a babbar tukunya wadda kika san za ta wadata ba zai zube ba. Ki dora kan wuta.

5- Idan kin ga ya fara alamun tafasa kamar haka, sai ki zuba rabin ruwan tsaminki ki ajiye rabin.

6- idan ya dan kara sai ki juye ragowar ruwan tsamin. Daga nan za ki ga yana dunkulewa wuri guda yana dan curewa.

7- sai ki nemi buhu ki kwashe na saman saboda zai hana shi tafasa yadda ya kamata.

8- Ga shi nan ya fara tafasa ya dunkule sosai.

9- Sai ki kwashe a cikin buhu ko mataci.

10- Sai ki daure buhun ki ajiye shi ya gama tsiyayewa na minti arba’in zuwa awa daya.

11- Daga nan sai ki cire ki juye a roba ko kuma tray. Shi ke nan kin gama.
