Ga yadda ake yam balls mu koya ‘yanuwa. Wannan recipe ne mai sauki da kuma dadi cikin ‘yan lokaci kadan uwargida za ki hada komai da komai.
Abubuwan hadawa
- Doya (dafaffafiyar doya)
- Nama (ki dafa sannan a daka shi )
- Flour
- Gishiri
- Kwai
- Tarugu
- Albasa (a jajjaga)
- Maggi (iya dandano da zai miki)
- Curry
- Kayan kamshi
- Man gyada (Na suya)
Yadda ake hadawa
- Ki dauko dafaffafiyar doyar ki kisa a turmi ki daka ta (sama sama dakan za ki yi) sai ki kwashe a kwano mai dan girma.
- Ki dauko dakakken naman ki kisa a cikin doyarki.
- Sai ki dauko jajjagen tarugunki da albasa ki zuba ciki
- Ki dauko kayan kamshi, gishiri kadan, curry, maggi ki sa a ciki.
- Sai ki juya sosai har sai ya hade jikinsa.
- Sai ki dauko kwanki ki fasa ki yanka albasa da tarugu a ciki (bana sa gishiri domin kwan ya kama jikin doyan sosai) ki ajiye a gefe.
- Ki tankade filawarki ki sa a tire ko roba ki ajiye shima a gefe.
- Sai kina diban hadin doyar ki ki na mulmula shi (ya mulmulu sosai), sai ki bade shi da filawa. Haka za kiyi da sauran hadin doyarki har ki gama.
- Sai ki daura man gyada akan wuta idan ya yi zafi sai kina daukan mulmulalliyar doyarki (wanda ki ka bade da filawa) ki na sawa a cikin kwanki (wanda ki ka buga ki ka yanka masa albasa da tarugu ciki) ki na sawa a mai ki na soyawa har ya soyu (golden brown). Haka za ki yi da sauran har ki gama da doyarki. Aci dadi lafiya.
Alhamdulillah
Thank uuu sister Allah y qara basira