Wannan vegetable rice din na da sauki wurin hadawa, haka da kudi kalilan za ki sarrafa ki yi ta ba tare da oga ya koka ba. A maimakon kullum mu yi ta yin shinkafa jollof, ko fried rice, ko mandi, to ga wata hanya ta sarrafa shinkafa mai tattare da sinadarai masu taimakawa jikin dan adam. Ku biyo mu dan ganin yadda ake hadata.
Abubuwan hadawa
1. Celery
2. Albasa
3. Mint leaves (na’ana)
4. Persly
5. Green beans
6. Carrot
7. Peas
8. Green pepper
9.Kayan dandano
10. Mixed spices.
11. Rice
Yadda ake hadawa
1. Da farko za ki dafa shinkafar ki da peas ki ajiyeta a gefe.
2. Sai kisa mai a tukunya, kisa albasa ki jujjuya ta har ta fara laushi.
3. Sai ki kawo spices da kayan dandano ki saka.
4. Ki kawo su carrot, persly da wannan celery din da na’ana da kika yanka su ki saka.
5. Sai ki kawo ruwa kadan ki zuba dan veggies din su dahu.
6. Sai ki dauko wanann shinkafar ki zuba a cikin hadin veggies din ki, ki jujjuya ko ina da ina ya hade. Shi kenan sai ki yi serving vegetable rice dinki.
Wannan recipe an koyar da shine a Ramadan Recipes 2025 Webinar wanda Chef Shaima Alhussainy ta gabatar.