Skip to content

Yadda ake vegetable rice

Share |
Yadda ake vegetable rice
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Mu koyi yadda ake vegetable rice cikin sauki. Wannan hadin shinkafa na bukatan kayan hadi guda bakwai ne da kuma steps guda biyar domin hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa
  2. Dankalin turawa
  3. Kwakwamba (cucumber)
  4. Tumatir
  5. Koren tattasai
  6. Jan tattasai
  7. Albasa

Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki fere dankalinki ki wanke ba tare da kin yankaba. Sai ki daura tukunya akan wuta ki sa ruwa idan ya yi zafi sai ki sa dankalin a ciki, ki sa gishiri kadan sai ki rufe nadan wani lokaci har sai ya nuna, sai ki dauke akan wuta ki tsane dankalinki a matsani yadan huce. A ajiye a gefe.
  2. Daura shinkafanki, sa gishiri kadan akan wuta idan ta tafasa ki wanke ta da ruwa sai ki kara maida ta kan wuta har sai ta dahu.
  3. Dauko kwakwambarki ki yanka (yankan kwakwamba mai round ya fi kyau), sannan ki dauko koren tattasai, albasa, tumatur da tattasai ki gyara, ki wanke, sai ki yanka su kanana sai ki kara wanke su ki tsane, ki tabbatar ya tsane ba ruwa a jiki. A ajiye a gefe.
  4. Sai ki dauko dafaffiyar dankalinki shima yanka shi kanana a jiye a gefe.
  5. Daga karshe sai ki dauko dafaffafiyar shinkafarki, ki zuba dafaffafen dankalinki tare da kayan veggies naki ki juya a hankali har sai sun hade da juna kamar yanda ki ka gani a hoton nan.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×