Skip to content

Yadda ake vegetable fried rice

Share |
Yadda ake vegetable fried rice
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake vegetable fried rice cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan fried rice ne mai dadi da za iya na gama gari ko na baki.

Abubuwan hadawa

  1. Perboiled rice (tafasasshen shinkafa)
  2. Nama (ki dafa)
  3. Tarugu
  4. Karas
  5. Koren wake
  6. Masarar gwangwani
  7. Peas (na yi amfani da na gwangwani)
  8. Ruwan silalenki
  9. Nama
  10. Gishiri
  11. Albasa
  12. Maggi (iya danganta da irin dandano ki)
  13. Kayan kamshi (spices)
  14. Butter

Yadda ake hadawa

  1. Ki gyara karas na ki, ki cire dattin bayan, sai ki yanka shi, ki yanka koren wake. Sai ki sami baking powder ki sa akai ki kawo tafasashshe ruwan zafi ki sa a kai ki rufe nadan wani lokaci.
  2. Idan sun yi laushi sai ki cire a ciki ruwan, ki sake wanke su da ruwa mai kyau ki tsane su a matsami sai ki ajiye a gefe.
  3. Dauko dafaffafen nama nan (dama ya huce) ki yanka shi kanana kanana. Sai ki yanka albasa ki ajiye a gefe shi ma. Ki dauko tarugu ki wanke ki jajjaga ko ki yanka kanana.
  4. Ki daura tukunyanki a kan wuta ki sa butter ki kawo albasa ki sa, sai ki soya sama sama. Ki kawo tarugu ki sa a ciki, ki soya sama sama shima, sai ki kawo naman ki sa a ciki ki dauko ruwan silalenki, da gishiri da maggi, da kayan kamshi da gishiri (iya yanda ki ke son dandano) sai ki juya a hankali ki kara ruwan zafi kadan inda zai iya dafa miki shinkafarki.
  5. Sai ki rufe tukunya har sai ya tafaso. Sannan ki dauko shinkafa ki zuba a ciki ki juya (idan baki so ta cabe ki rage ruwan a hadinki a wani kwano daban sai ki zuba rabin shinkafa tare da albasa a cikin tukunya ki juya da mara, sai ki zuba ragowan shinkafa da ragowan ruwan hadinki tare da ragowan albasar ki juya da mara a hankali).
  6. Ki dauko leda ko foil paper ki rufe saman shinkafa (yin hakan yana hana ta yi dahuwan gefe daya) ki rufe tukunya da marfi nadan wani lokaci har ruwan ciki ya shanye. Sai ki bude ki zuba karas na ki da koren wake, da peas, da masarar gwangwani a ciki ki juya a hankali ki rufe tukunya sai ki rage wuta sosai.
  7. Ki barshi nadan wani lokaci (su turaru) sai ki sauke. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×