Skip to content

Yadda ake vegetable bread rolls

Share |
yadda ake vegetable bread rolls cikin 6 steps
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Ku karanta yadda ake bread rolls mai dadi da laushi.

Abubuwan hadawa

  1. Bread (irin na N200 – N250)
  2. Butter
  3. Kwai dafaffafen (ki yanka kanana)
  4. Dankali dafaffafe (ki yanka Kanana)
  5. Dafaffafen nama (ki yanka shi Kanana)
  6. Tarugu (ki jajjaga)
  7. Albasa (ki yanka)
  8. Latas (ki gyara ki wanke)
  9. Lawashi
  10. Kayan kamshi
  11. Maggi (iya dandano da zai miki)
  12.  

Yadda ake hadawa

  1. Ki sami non stick pan naki kisa a wuta sai ki sa butter kadan, idan ya narke ki sa jajjagen tarugunki da albasa ki soya sama sama, ki kawo yankakken namanki ki sa a ciki ki juya.
  2. Sai ki kawo kayan kamshi, maggi iya dandano da zai miki, ki kawo dafaffafen dankali ki ki sa, dafaffafen kwai da lawashi ki sa sai ki sa ruwa kadan kamar cikin cokalin cin shinkafi biyu. Sai ki juya ki rufe pan naki nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye. ki ajiye a gefe
  3. Ki dauko bread naki ki sami wuka (ta yankan bread) ki yanyanke gefe gefe bread (ki yi trimming edges din) ya zama iya zalla bread (farin ciki) ne za ki yi amfani dashi.
  4. Sai ki dauki wukan ki yankashi a tsaye, ki sami kwalba ko rolling pin ki murja shi har sai ya zama fale-fale. Haka za ki yiwa sauran bread din ma.
  5. Sai ki dauko bread (wanda ki ka yi fale-fale dashi) ki shinfida latas a ciki, sai ki dauko hadin su namanki ki sa daga dungun bread din sai ki mishi nadin tabarma ki ajiye a gefe. Haka za kiyi da sauran har ki gama da su.
  6. Sai ki dauko butter ki shafa a jikin bread ki (wanda ki ka yi masa nadin tabarma) ki gasa a non stick pan. Amma ki rika juyawa dan kar ya kone ta gefe daya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake vegetable bread rolls”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×