Skip to content
Share |
yadda ake tsiren tukunya

Ku koyi yadda ake tsiren tukunya. Wannan tsiren tukunya yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

 1. Jan nama kilo
 2. Albasa 1
 3. Maggi 4
 4. Yajin barkono 1/2 cokali
 5. Kuli kuli (gari)
 6. Kayan kamshi
 7. Man gyada ludayin miya
 8. Koren tattasai 2

Yadda ake hadawa

 1. Da farko zaki wanke namanki ki masa yanka mai fadi-fadi ki ajiye a gefe.
 2. Sai ki hada yajin da man gyada da garin kulikulinki ki sa maggi da kayan kamshi sai ki kwaba.
 3. Sai ki dinga shafawa a jikin naman gaba da baya.
 4. Idan kin gama sai ki kawo tukunya ko kasko (frying pan) mara kamu sai ki jera ki dora a wuta ki rufe ki barshi. Kar ki sa wutar tayi yawa.
 5. Sai ki ringa juyawa, idan yayi sai ki sauke ki  yanka dai dai misali kisa sa pilet ki yanka albasa da koren tattasanki.
Add to Lists (0)

No account yet? Register

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page