Skip to content

Yadda ake toast bread na musamman

Share |
yadda ake toast bread na musamman
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake toast bread mai dadi ga kuma kyau. Wannan toast bread na musamman yana da saukin hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya.

Abubuwan hadawa

  1. Bread mai yanka (ko ki saya irin na 200 ki cire gefe gefe ki yanka)
  2. Butter
  3. Nikakken nama (naman gwangwani)
  4. Kwai dafaffe
  5. Karas (ki gurza)
  6. Albasa
  7. Tarugu
  8. Kayan kamshi
  9. Mai
  10. Maggi

Yadda ake hadawa

  1. Ki yanke gefe gefen breadin ki sai ki shafa butter a gefe daya haka za ki yi har sai kin gama da breadinki. Ajiye a gefe.
  2. Daura kasko kan wuta ki sa mai kadan ki kawo tarugu da albasa ki sa ki juya sannan ki kawo namanki (na gwangwani) ki sa, sai ki juya ki kawo kayan kamshi, maggi iya dandanon da zai mi ki, ki sa sannan ki juya kidan bar shi nadan wani lokacin (amma ki rage wuta) sai ki sauke. Ajiye a gefe.
  3. Dauko breadinki (wanda ki ka shafa masa butter) sai ki juya ta inda baki shafa masa butter ba ki kawo namanki, ki zuba sannann ki danna naman da cokali (domin ya kama jikin breadin) ki kawo albasa, kwai da karas ki shirya a hankali akan naman.
  4. Sai ki dauko barin breadin ki rufa inda baki shafa butter a kai ba. Haka za ki yi har sai kin gama da sauran.
  5. Daura non-stick pan akan wuta idan ya yi zafi ki kawo hadin breadin ki ki sa ki gasa shi gaba da baya har sai ya gasu. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake toast bread na musamman”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×