Uwargida ki koyi yadda ake toast bread da veggies. Wannan toast bread da veggies yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Biredi mai yanka
- Nama(dafaffe)
- Butter ko mai
- Kayan kamshi
- Tarugu (ki jajjaga)
- Albasa (ki yanka)
- Kabeji (ki yanka)
- Karas (ki yanka)
- Koren wake (ki yanka)
Yadda ake hadawa
- Ki dauko naman ki ki sa a turmi ki daka ki kwashe ki ajiye a gefe.
- Dauko kasko ki sa butter ko man gyada kadan sai ki yanka albasa ki soya sama sama, sannan ki kawo tarugu ki sa ki juya.
- Sai ki dan zuba ruwa kadan sannan ki kawo nama (wanda ki ka daka) ki sa ki juya.
- Sannan ki sa maggi da gishiri (iya dandanon da zai miki) kayan kamshi ki sa, sai ki juya ki rufe nadan wani lokaci.
- Daga karshe ki kawo su kabeji, da karas, da koren wake ki zuba ki rufe su dan turaru sai ki sauke ki ajiye a gefe.
- Dauko biredinki mai yanka ki shafa masa butter a gefe daya (haka za ki yi shafe jikin sauran biredin gefe daya daya) ajiye a gefe.
- Sai ki dauko abun gashi (toaster machine) sai ki dauko biredi (wanda ki ka shafa masa butter ta gefe daya) ki fara daura gefen da kika shafawa butter ta kasa.
- Sannan ki hadin nama ki ki zuba cikin biredin (ki daidaita shi tagun ramin guda biyu su zaki sawa hadin nama banda tsakiya).
- Sai ki dauko wani biredin ki rufe shi ta inda ba butter sai ki gasa haka za ki yi tayi har sai kin gama. A ci dadi lafiya