Skip to content

Yadda ake stuffed potato nuggets

Yadda ake stuffed potato nuggets
4
(8)

Mu koyi yadda ake stuffed potato nuggets cikin sauki. Wannan potato nuggets yana da dadi sosai za a yi yin shi domin yara ko kuma baki.

Abubuwan hadawa

  1. Dankalin turawa
  2. Nikakkiyar nama
  3. Albasa
  4. Tattasai
  5. Attarugu
  6. Maggi
  7. Kayan kmashi
  8. Turmi da tabarya
  9. Mai

Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki bare dankali ki dafa shi daban.
  2. Sai ki daka ki ajiye a gefe.
  3. Ki yanka albasa, sannan ki dan soya sama sama, sai ki kawo nama ki saka, ki kawo jajjagen tarugu da tattasai da kayan kamshi ki saka ki gauraya sannan ki sa maggi ki rufe, sai ki bari har ya tsane ruwansa ya yi dai dai.
  4. Sai ki rika diban  dankali da ki ka dafa ki na fadadawa a hannunki ki na zuba naman a ciki, ki rika mulmula wa har ki gama.
  5. In kin gama sai ki soya su a cikin mai maizafi.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×