Ku koyi yadda ake spicy cucumber salad cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi bakwai ne da steps hudu kacal.
Abubuwan hadawa
- Cucumber
- Tumatur
- Albasa
- Koren tattasai
- Sauce na tarugu da albasa
- Soyayyen plantain
- Dafaffafen kwai
Yadda ake hadawa
- Ki sami cucumber ki wanke ki yanka. Ajiye a gefe.
- Dauko koren tattasai ki gyara ki yanka tare da tumatur na ki da albasa, kwai shima ki yanka.
- Dauko kwano ki zuba cucumber ki a ciki sai ki kawo albasa, tumatur, koren tattasai, dafaffafen kwai, soyayyen agada ki sa.
- Daga karshe ki kawo sauce na tarugunki da albasa ki sa a ciki kadan sai ki juya su hade jikansu sai ki diba ki zuba a gefen abinci kamar shinkafa da miya, jollof da dai sauransu.
Karin bayani
Kina gamawa ki sa a fridge don cucumber salad ba ya jimawa (soba da nan danan za ki ga ya fara fidda ruwa a jikinsa). A ci dadi lafiya.
Aslm
Aslm
Wa’alaikum salam