Skip to content

Yadda ake special fruits combo

Share |
Yadda ake special fruits combo
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Mu koyi yadda ake special fruits combo. Wannan hadin fruits ne mai armashi da kuma tarin karin lafiya cike cikinsa. Ku gwada mu ji yadda aka yi!

Yadda ake hadawa

  1. Mangoro ja
  2. Mangoro Kore
  3. Strawberry (faraula)
  4. Apple (tuffa) ja da kore
  5. Abarba
  6. Gwanda
  7. Pear
  8. Sugar syrup (sugar ake narkarwa cikin ruwa a daura kan wuta har sai ya yi kauri)

Yadda ake hadawa

  1. Da farko za a wanke duk kan kayan marmarinda muka ambata a sama sai ayayyanka su da kyau yadda girman kowani yanka zai zama dai dai.
  2. Bayan angama yankawa sai a kawo narkakkiyar suga a zuba akai a cakude ko ina ya ji, a saka  cikin fridge ya yi sanyi.

In ya yi sanyi a dauko a rika ci da cokali ya yin hutawa ko kan a ci abinci ko bayan an ci abinci.

Ga masu ciwo diabetes za a iya sa musu zuma a maimakon sukari.

Ina son wannan combo yayin da na ke karatu, ina dan duba littafai na, ina kuma cin kayan marmari na. Ya Allah mun gode maka, Allah kar Ka haramta mana cin kayan marmarin  aljanna. Ya Allah muna rokonKa Ka samu aljannarka madaukakiya da rahmarKa ya Arhamarrahimiin.

Rate the recipe.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading