Skip to content

Yadda ake special cin cin

Share |
Yadda ake special cin cin
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake special cic cin cikin dan kankanin lokaci. Wannan cin-cin yana da dadi da kuma saukin hadawa. Ku gwada ku bamu labari.

Abubuwan hadawa

 1. Flour kofi shida
 2. Butter daya
 3. Sugar kofi biyu
 4. Madarar gari cokali biyar da rabi
 5. Baking powder cokali daya da rabi
 6. Bawon lemon tsami cokali daya
 7. Cinnamon quater na cokali
 8. Gyadar miya guda biyu
 9. Kwai biyar
 10. Gishiri kadan
 11. Ruwa
 12. Vanilla flavour kadan

Yadda ake hadawa

 1. Ki tankade flour ki sa a roba, ki sa baking powder, sugar, Cinnamon (powdered), gyadar miya ki bare ki daka sai ki sa, ki sa gishiri, bawon lemon (lemon zest), sai ki juya su hade.
 2. Ki buga kwai ki sa, ki sa madara, vanilla flavour sai ruwa kadan ki kwaba dough ki yi kneading bayan ya hade sai ki raba kashi uku. 
 3. ki dauko chopping board ko tray ki sa kashi dayan kiyi rolling sai ki yanka da cutter haka za ki yi wa sauran dough din, wanda ki ka yanka ya rage shima za ki kara kneading ki yi rolling ki yanka.
 4. Ki daura mai a wuta ki sa albasa kadan ki soya mai na ki sai ki sa cin cin ki soya.

Karin bayani

 1. Sai mai na ki ya yi zafi sannan ki soya in ba haka ba zai sha miki mai.
 2. Idan mai ya yi zafi sannan ki ka soya yafi kyau amma bawai za ki bari man ya yi mugun zafi bane kuma don zai kone.
 3. Bayan kin dama madarar ki da ruwa, kin kwaba dough idan da bukatar ruwa sai ki kara.
 4. In ba ki da chopping board za ki iya using clean flat surface. Cutter kuma duk shape da ki ke so sai ki yi amfani da shi.
 5. Idan ki na so ki yi dogo dogon cin cin bayan kin gama kwabi sai kiyi rolling ki dauki wuka ki yanka ta dogo dogo (horizontally), sai ki zo ki yanka ta sau biyu vertically, sannan ki soya.

Akwai wanda ake yi da engine na taliya ya fi fita even ga yadda za ki yi

 1. Ki kwaba normal Dough na ki sai ki raba shi gunduwa gunduwa kamar za ki yi dubulan. Sai ki dauko daya ki sa a tsakiyan engine na taliya wajen da ake murza dubulan bayan ya fito (na farkon yana fita da kauri sosai).
 2. Sai ki sake canza number ki sake yi wannan karon zai fita mai kyau sai ki sa a space na inda ake taliya ki winding zai fito kamar taliya sai ki raba sau biyu ko uku yanayin dogon da ki ke so.

Rate the recipe.

Average: 1.2 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake special cin cin”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading