Skip to content

Yadda ake spaghetti jollof cikin sauki

Share |
Yadda ake spaghetti jollof 2
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Cikin sauki, mu koyi yadda ake spaghetti jollof.

Abubuwan hadawa

  1. Tafasashshe taliya
  2. Dafaffafen nama (ki yanka kanana)
  3. Cray fish (ki nika)
  4. Tarugu
  5. Tattasai
  6. Albasa
  7. Gishiri kadan
  8. Koren tattasai
  9. Lawashi (ki yanka)
  10. Ganyen curry (ki yanka)
  11. Kayan kamshi
  12. Maggi
  13. Tumatur
  14. Albasa

Yadda ake hadawa

  1. Gyara tarugunki da tattasai ki markada ya markadu, dauko tumatur, koren tattasai, albasa ki yanka su sai ki ajiye a gefe.
  2. Daura tukunyanki akan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama sai ki dauko markadadden kayan miyanki zuba a ciki ki juya ki rufe nadan wani lokaci.
  3. Sai ki kawo nama ki zuba a ciki ki juya ki kawo maggi ki sa iya dandano da zai miki, kayan kamshi ki sa, gishiri kadan, cray fish ki sa, ki juya ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin.
  4. Sai ki kawo ruwan zafi dan dai dai ki sa (wanda zai karasa dafa miki taliya) ki rufe tukunya idan ya tafaso sai ki kawo tafasashshen taliya ki zuba a ciki ki juya a hankali ki rufe sannan ki rage wuta.
  5. Bayan dan lokaci kadan sai ki dauko lawashi, ganyen curry, zuba ki rufe su turaru, daga karshe sai ki dauko tumatur, albasa, koren tattasai ki zuba ki juya a hankali sai ki sauke. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

5 thoughts on “Yadda ake spaghetti jollof cikin sauki”

  1. ᗰᗩՏᕼᗩ ᗩᒪᒪᗩᕼ ᗰᑌᑎᗩ ᘜOᗪIYᗩ ՏOՏᗩI ᗩᒪᒪᗩᕼ Yᗩᑫᗩᖇᗩ ᗷᗩՏIᖇᗩ Kᑌᗰᗩ Iᑎᗩᗷᗩ ᗪᗩᗰᑌᗯᗩ ᙭ᗩᑎ IYᗩ Տᗩᗰᑌᑎ ᑎᑌᗰᗷᗴᖇᑎ ᗯᗩYᗩᑎKI ᑭᒪՏ

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×