Skip to content

Yadda ake spaghetti jollof

Share |
Yadda ake spaghetti jollof
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Uwargida ki koyi yadda ake hada spaghetti jollof gangariya. Wannan spaghetti ana hada shi ne da kayan hadi guda tara cikin matakai biyar!

Abubuwan hadawa

  1. Tafasashshe taliya
  2. Kifi banda
  3. Kayanmiya (ki markada)
  4. Alaiyaho (ki gyara ki wanke basai kin yanka ba)
  5. Albasa (ki yanka)
  6. Kayan kamshi
  7. Man gyada
  8. Maggi
  9. Cucumber (ki yanka)

Yadda ake hadawa

  1. Daura tukunyarki a kan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama. 
  2. Sai ki kawo markaden kayan miya ki zuba a ciki, ki barshi ya yi ta tafasa har sai ruwan ya kusa shanyewa sai ki kawo kayan kamshi, maggi iya dandano da zai miki ki sa gishiri kadan ki sa sai ki juya.
  3. Sai ki kawo kifi banda ki sa a ciki (ki tabbatar kin bareshi kin cire mashi kaya, ki jika da ruwan zafi nadan wani lokaci) Ki kara ruwa kadan (iya wanda zai karasa dafa miki taliya ki).ki zuba kullin rufe tukunya nadan wani lokaci har sai ruwan ya tafasa.
  4. Sai ki kawo tafasashshe taliya ki zuba a ciki ki juya a hankali ki rufe tukunyarki na dan wani lokacin.
  5. Daga karshe, sai ki kawo alaiyaho ki zuba a ciki ki juya ki rufe tukunyarki su turara sai ki sauke ki zuba a plate ki kawo yankakken cucumber ki sa a kai, idan akwai soyayyen nama ki sa akai. A ci dadi lafiya

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

2 thoughts on “Yadda ake spaghetti jollof”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×