Mu koyi yadda ake soyayyen dankali da kwai . Wannan soyayyen dankali da kwai yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Dankalin turawa
- Kwai (3)
- Man gyada
- Albasa (1)
- Attarugu (2)
- Tumatur (2)
- Maggi (2)
- Gishiri
Yanda ake hadawa
- Da farko dai uwargida za ki fere dankalinki ki yanka dogo-dogo.
- Sai ki dora kaskonki a wuta ki sa manki yayi zafi sai ki dauko dankali kisa gishiri kijuya kisa a man. Karki yawaita juyashi zai fashe.
- Idan yayi sai ki tsame amatsami. Yayin da man jikin dankalin ya dige, sai ki sa a kwano mai kyau ki ajiye a gefe.
- Bayan nan sai ki dauko kwano mai kyau ki fasa kwanki.
- Sai ki yanka albasarki da attarugu da tumatur, yanka kanana ki zuba a cikin kwai din, sannan ki sa maggi sai ki kada ya kadu sosai.
- Sai ki dora kaskonki a wuta ki sa mai kadan ki soya sai ki dora kan dankalinki.
Sai a baiwa maigida da yara su yi buda baki da shi. Na gode