Skip to content

Yadda ake soft peanut and coconut balls

Yadda ake soft peanut and coconut balls
1.8
(5)

Ku koyi yadda ake soft peanut and coconut balls. Ana bukatan kayan hadi guda shida ne da kuma steps biyar domin hada wannan recipe.

Abubuwan hadawa

  1. Gyada kofi1
  2. Kwakwa kofi ½
  3. Sugar kofi ¾
  4. Madara ta gari cokali 3 babba
  5. Man gyada ko butter cokali 1
  6. Ruwa cokali 1

Yadda ake hadawa

  1. Ki gyara gyadan ki kidan cire bawon jikin, sai ki daka a turmi sama sama, ajiye a gefe.
  2. Dauko kwakwa ki cire bakin jikin, sai ki gurza shi a jikin abun goge kubewa, say ki ajiye a gefe.
  3. Ki daura non stick pan naki akan wuta (ki rage wutan) ki sa sugar sai ki na juyawa a hankali har sai sugar ya narke.
  4. Sai ki kawo ruwa ki sa ki juya, ki kawo man gyada ki sa ki juya sai ki dauko gyada ki zuba ki kawo kwakwa ki sa ki juya, sai ki kawo madara ki sa ki juya ki kashe wutanki.
  5. Ki shafa mai a jikin faranti sai ki juye hadin ki ki yi rolling na shi, sai ki na diban kadan kadan ki na mulmula da tafin hannu ki. A ci dadi lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×