Mu koyi yadda ake skewers na dankali mai dadi da sauki, abubuwan hadawa guda tara, matakai guda hudu kacal.
Abubuwan hadawa
- Dankalinb turawa
- Tumatiri
- Koriyan tattasai
- Tsinken tsire
- Maggi
- Curry
- Kayan kamshi
- Mai
- Attarugu da tattasai
Yadda ake hadawa
- Da farko ki bare dankali ki daura kan wuta ya dahu amma ba lugub ba. Ki tsane ki ajiye a gefe.
- Ki hada maggi da gishiri curry kayan kamshi da mai da jajjagen attarugu da tattasai ki shafe dankali dashi ko ta ina.
- Sai ki kawo tsinken tsirenki ki sa dankali sai ki kawo tumatiri ki sa sai ki kawo koriyan tattasai ki sa sannan ki kawo dankali ki sa, haka za ki yi ta jerawa har ki gama.
- In kin gama sai ki sa a abin gashi ki gasashi yadda zai tsane hadinsa yashiga jikin sa.