Skip to content

Yadda ake sinasir

yadda aake sinasir
3.5
(6)

Ku koyi yadda ake sinasir. Wannan sinasir din yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa ta tuwo kofi 2
  2. Albasa 2
  3. Suga kadan
  4. Yeast chokali 2 babba
  5. Nono idan kina bukataba
  6. Mangyada
  7. Gishiri

Yadda ake hadawa

  1. Da farko zaki sami shinkafarki ki wanke ta ki jika ta.
  2. Idan ta kwana sai ki kai inji a markada miki. Kar a markada miki akan wake.
  3. Idan aka kawo sai ki zuba yeast ki bubbuga ta sai ki rufe ki ajiye a waje mai dumi.
  4. Idan ta dan jima sai ki zuba suga da gishiri kadan da nono kadan don yana kara kyau da tashi.
  5. Sai ki yanka albasarki kanana ki zuba a ciki.
  6. Sannan sai ki dauko farantin suya mara kamu ki dora a wuta sai ki dinga zuba manki kuma ki dinga zuba kullun shinkafarki, sai ki sa marfi ki rufe. Ba a juyawa. Idan ya soyu sai ki cire. Haka zaki yi tayi harki gama.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×