Skip to content

Yadda ake simple fruit salad

Share |
Yadda ake simple fruit salad
Add to Lists (0)

No account yet? Register

Mu koyi yadda ake simple fruit salad cikin sauki. Ana bukatan abubuwa guda shida ne domin hada wannan fruit salad cikin steps guda biyar.

Abubuwan hadawa

 1. Kankana (yankan naira dari)
 2. Abarba 2 (yankan naira dari)
 3. Lemon zaki 3
 4. Lemon tsami 1
 5. Foster clerk cokali 1
 6. Kaninfari guda 5

Yadda ake hadawa

 1. Ki dauko abarba ki wanke ki cire wannan baki bakin ramin dake jikin ta sai ki yanka ta kanana sosai ajiye a gefe.
 2. Kankana shima wanke ki cire bawon bayanki yanka shi kanana ki na cire wannan bakaken kwallayen da ke ciki sai ki ajiye gefe.
 3. Ki bare bayan lemon zakinki, sai ki cire cikinsa ki na cire farare kwallon ciki ajiye a gefe.
 4. Ki dauko kwano maidan girma sai ki juye duka abubuwan da kika yanka a ciki ki juya sosai. Sai ki dauko foster clerk na ki ki sa a ciki ki juya.
 5. Sannan daga karshe ki yanka lemon tsami ki matse a ciki ki Jefa har da bawon. Sai ki kawo kaninfari ki sa sai ki sa a fridge ya yi sanyi sosai. Sannan idan kinzo zubawa za ki sha sai ki cire bawon lemon tsami tare da kaninfari a ciki ki zubar (amfanin sa shi shi ne zai karawa fruits salad na ki kamshi mai dadi sosai).

Karin bayani

Za ki iya kara ruwan sanyi a ciki idan kinga bai miki ruwa ba (amma kadan ake sawa). Sannan idan ba ki da foster clerk za ki iya amfani da suga. 

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×