Skip to content

Yadda ake simple cucumber garnish

Yadda ake simple cucumber garnish
5
(1)

Mu koyi yadda ake simple cucumber garnish cikin sauki, abubuwan hadawa guda hudu, matakai guda hudu kacal.

Abubuwan hadawa

  1. Kwakwamba (cucumber mai kyau marar mayan ‘ya’ya a ciki)
  2. Carrot
  3. Wuka mai zigzag
  4. Pipe (wannan bakin ko farin silver karfen labule wanda ake sa labule a jiki)

Yadda ake hadawa

  1. Ki wanke kwakwambarki, sai ki yanke saman kadan ki sai ta pipe naki a tsakiyan cucumber sai ki dinga dannawa a hankali har sai kin Kai karshe (ki tabbatar kina danna shi a hankali kuma a tsakiya kike tafiya).
  2. Bayan kin kammala sai ki zaro pipe naki a hankali za ki ga ya baki rami a tsakiyan sai ki a jiye a gefe.
  3. Ki sami carrot madaidaici (wanda zai shiga tsakiyan cucumber ki) sai ki cire dattin bayan sai ki wanke sannan ki danna shi a tsakiyan cucumber a hankali har sai kin kai karshe.
  4. Ki dauko wukan ki (mai zigzag) ki yanka shi kamar yanda ki ka ga ni a hotonnan. Sai ki daura akan salad ko abinci kamar su jollof, ko su fried rice da sauran su. A na amfani da shi a wajeje da dama.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×