Mu koyi yadda ake simple cucumber garnish cikin sauki, abubuwan hadawa guda hudu, matakai guda hudu kacal.
Abubuwan hadawa
- Kwakwamba (cucumber mai kyau marar mayan ‘ya’ya a ciki)
- Carrot
- Wuka mai zigzag
- Pipe (wannan bakin ko farin silver karfen labule wanda ake sa labule a jiki)
Yadda ake hadawa
- Ki wanke kwakwambarki, sai ki yanke saman kadan ki sai ta pipe naki a tsakiyan cucumber sai ki dinga dannawa a hankali har sai kin Kai karshe (ki tabbatar kina danna shi a hankali kuma a tsakiya kike tafiya).
- Bayan kin kammala sai ki zaro pipe naki a hankali za ki ga ya baki rami a tsakiyan sai ki a jiye a gefe.
- Ki sami carrot madaidaici (wanda zai shiga tsakiyan cucumber ki) sai ki cire dattin bayan sai ki wanke sannan ki danna shi a tsakiyan cucumber a hankali har sai kin kai karshe.
- Ki dauko wukan ki (mai zigzag) ki yanka shi kamar yanda ki ka ga ni a hotonnan. Sai ki daura akan salad ko abinci kamar su jollof, ko su fried rice da sauran su. A na amfani da shi a wajeje da dama.