Ga wani dabaran yadda ake sauce na plantain mai dadi da kuma sauki. Cikin kalilan lokaci, uwargida zaki iya hada wannan lafiyayyen sauce.
Abubuwan hadawa
- Plantain
- Dankalin turawa (Irish potato)
- Tumatir
- Albasa
- Karas
- Dafaffiyar koda
- Attarugu
- Koren tattasai
- Tumeric
- Maggi
- Seasoning of choice
- Mai
- Gishiri
Yadda ake hadawa
- Da farko ki bare dankalin turawan, ki yanka shi kanana sai ki tafasa ki ajiye ta a gefe.
- Plantain shima ki bare ki yanka kanana za ki iya dan motsawa a cikin mai (soyawa sama sama).
- Sai ki daura pan a wuta ki sa mai, da albasa, da tumatir, da attarugu, da koda, da maggi, da seasonings, sannan gishiri kadan, da tumeric sai ki dan motsa su.
- Ki zuba dankalin turawa da koren tattasai kidan motsa sai ki sa plantain ki sake dan motsawa na wani lokaci sai ki sauke shikenan.
Karin bayani
- Idan baki soya plantain na ki sama sama a mai ba kar ki yawanta juyawa a cikin sauce dan zai narke.
- Za ki iyayin sauce din da plantain zalla ko irish potatoes (dankalin turawa) zalla in kina so.
- Za ki iya cin plantain sauce da farar shinkafa, spaghetti, macaroni, couscous, ko da chips.