Mu koyi yadda ake sarrafa egg muffin cikin sauki, abubuwan hadawa guda bakwai, matakai guda uku.
Abubuwan hadawa
- Kwai
- Koriyan tattasai
- Tattasai 1
- Attarugu 1
- Albasa
- Abin gasa cake (cupcake papers & muffins)
- Oven
Yadda ake hadawa
- Za ki fasa kwai, ki yanka albasa sannan ki yi jajjagen tattasai da koriyan tattasai da attarugu ki zuba a ciki.
- Ki sa maggi sai ki kada su gaba daya.
- Sai ki samo fefan sawa a cake ( cupcake paper). Ki shafe shi da mai. Sai ki zuba hadin kwan a ciki sai ki sa a abin saka su kafin ki sa a oven. Sai ki gasa har sai ya yi.
Yana da dadi sosai. Ana iya ci da dankali ko plantain ko doya. Ni dai da dankali nafi so. Na gode. Sai mun hadu a girki na gaba.