Da yawan mutane sun iya yin samosa, sai dai da yawa ba su iya yin wraps din da kansu ba. Wasu sai dai su saya su karasa hada samosar a gida. Wasu kuwa saboda yana yi masu wahala sun gwammaci su sayi frozen one, suya kawai za su yi. A yau na zo maku da yadda za ku yi samosa wraps da kanku tare da shawarwarin yadda za ta fita lafiya ba tare da ta harhade ba, ko kuma ta sha mai ko dai wata matsalar. Measurement din da zan kawo maku zai ba ku 50-55 pieces na wraps din nan. Sirri ne zan kawo maku wanda da kudinku ma ba lallai a fada maku shi ba.
Abubuwan bukata
1- 4 cups flour
2- 2 tablespoons vegetable oil
3- 1 teaspoon salt
4- 1 cup water
5- 1/2 extra cup of flour (wanda ake sprinkling a kan wraps)
6- 1/2 cup extra vegetable oil (wanda za a shafa a kan wraps din)
Yadda ake yi
1- Ki zuba flour a bowl, ki zuba gishiri, mai, sai ki kawo ruwa ki zuba amma ba duka ba. Kina yayyafawa a hankali kina motsawa har sai ya ba ki perfect dough. Amma ba sticky one ba.

2- Daga nan ki lullube da leda ki bar shi ya yi resting na minti biyar zuwa goma.

3- Sai ki cuccura shi kanana amma ba sosai ba. Idan kina da measuring scale ki auna kamar 25-30g each.

4- sai ki luliye shi da kyau kamar yadda na yi a wannan hoton.

5- Ki yi amfani da rolling pin ki yi flattening dinsa amma ba da fadi sosai ba. Kuma ki tabbata sun zama equal sizes.

6- ki dauki guda daya ki yi amfani da silicon brush ki shafa mai a kai.

7- Idan kin shafa mai da kyau sai ki barbada flour kuma.

8- Sai ki kara dauko wani guda ki dora a kai. Kina iya hada guda uku ko kuma ki bar shi guda biyun kafin ki gwanance sosai.

9- Ki kama bakinshi ki hade da kyau, sannan ki yi flattening dinsa sosai sai ya yi fadi.

10- Daga nan ki dauka ki dora a kan non stick pan mai fadi. Kar ki zuba mai ko kadan.
11- idan dayan gefen ya yi za ki ga yana fitar da air bubbles alamar ya yi ke nan sai ki juya dayan gefen ma. Za ki saka wuta very low dan kar ya kone.

12- Idan kin gama duka sai ki samu rounded plate ko murfin tukunya ki saita sannan ki yanka shi da pizza cutter ko kuma knife.

13- Then ki daidaita tsakiya ki raba shi biyu.
14- Ki kara yanka shi zai zama 4 ke nan.

15- Ga shi nan bayan an gama yankawa.

16- Sai ki kama a hankali ki raba shi. Kada ki saka gaggawa don ba wuya zai iya yagewa.

17- Shi ke nan sai ki yi packaging. Za ki iya saka shi a freezer zai kai wata daya ko ma fin haka in dai ya yi kankara.
18- Har business ma za ki iya yi da shi.

Dalilan da ke hana samosa zama crispy. Wato wannan kayau kayau din. Wasu idan sun yi ba ta yi. Kuma ina yawan samun wadannan tambayoyin.
1- rashin zuba mai a cikin kwabi
2- ya zama filling din ya huce sosai. Idan kika sauke daga wuta ki bari ya huce tsaf sannan ki fara nadin samosar. Idan ba haka ba zafinshi zai huda wraps din, kuma zai hana shi crispy ne.
3- ki tabbata filling din ya tsane tsaf babu ruwa a cikinsa. Idan da ruwa kina zubawa a samosa zai jika ta. Za ta yi losing crispness.
Dalilan da suke sanya ko an yi storing ba za a samu good result ba.
1- ko dai sai da ya yi kwanaki kafin a saka a freezer
2- ko ya zama very thick. As in bai yi lakai-lakai ba, ya yi kauri da yawa. Hakan zai sanya shi kakkaryewa a lokacin da aka ciro shi daga freezer
3- ko kuma bayan an ciro daga freezer ba a bar shi ya sake jikinsa ba
4- ko wurin packaging bai nade da kyau ba sai ruwa ya shiga ciki
Dalilin da ke sanyawa samosa ta yi bubbles idan an soya, ma’ana ta yi kwayaye. Kodayake wannan ba wani laifi ba ne, wasu bai dame su ba wasu kuma yana damun su har su dinga tambayar wai me ya sa idan sun soya samosa take yin wannan kwayaye?
Dalilin shi ne, da kika zuba mai kika dora a wuta, kin bar shi ya yi over heating, bi ma’ana ya yi zafi da yawa ta yadda kina zuba samosar duk za ta fitar da kwayaye.
Dalilin da ke sanya samosa karyewa kafin a soya.
Wannan yana samuwa ne a lokacin da kika yi storing dinsa. Yana da kyau kada ki zuba da yawa a cikin leda. Idan kin tashi ki zuba adadin da kika san za ki soya a lokaci guda. Ta yadda ko kin zuba a cikin mai zai kwashe duka ba dole sai kin raba su ba. Kuma kada ki bari sai ta huce. A yadda take kankaren nan za ki sanya cikin mai ki soya.
Dalilan da ke sanya samosa shan mai yayin soyawa.
1- idan a freezer kika sa, ba ki da bukatar tsayawa sai ta narke. Ki sanya ta kankararrar a mai, da kanta za ta rabe musamman idan kina dan juyawa a hankali. Amma kika bari ta narke za ta sha miki mai sosai.
2- zuba samosa da yawa a cikin mai, yana sanya man ya huce, samosa ta shake shi tsaf a jikinta.
3- wuta low ma tana sanya samosa shan mai. Ba a ce ki saki wutar da yawa ba, amma dai ya zama medium low flame.
Dalilan da suke sanyawa samosa ta bude a lokacin soyawa
1- bai nadu da kyau ba tun farko
2- ba ki shafa flour paste (kwabin flour) da kyau ba.
3- kwabin flour paste din ya yi ruwa
4- wraps din sun bushe. Idan hakan ta faru to lallai ko kin shafa flour paste ba lallai ya zauna ba. Karshenta yana shiga mai zai bude ne.
5- idan wrap ya cika karfi da yawa, bi ma’ana ya yi kauri, shi ma yana hana shi kama flour paste d akyau, kuma yana shiga mai za ku ga ya bude.
Dalilan da suke sanya wa ya qi rabuwa da kyau duk ya manne ko kuma ya baci.
1- ko ruwa ya yi wa dough yawa
2- ko mai bai wadata ba wurin shafawa
3- ko an saka hanzari wurin rabawar ba a bi a hankali ba duk zai lalace.
4- aikin nutsuwa ne. Dole ne sai kin sanya nutsuwa tun daga farkon wraps din har karshe
5- ko wani wuri bai gasu ba, flour ta zama danya-danya shi ma yana hana shi rabuwa da kyau. Don haka a bari ya gasu har sai kin ga yana fitar da wannan air bubbles (kwayaye) alamun har ciki ya gasu kenan.
6- kar ki sakar masa wuta da yawa, zai kone, kuma a karshe ya qi rabuwa.
7- kar ki bari ya bushe, idan har ya bushe shi zai sanya kina rabawa yana karyewa.
8- kar ki bari ya jike, ko da kuwa da zufa ne. Ki kiyaye, abu mafi kyawu shi ne ki samu kitchen towel kina yi kina lullubewa. Kin ga ba zai bushe ba, ba kuma zai jike ba.
9- a matsayinki ta ‘yar koyo, ko kuma wacce za ta fara yanzu, ko wacce ba ta jima da farawa ba, kar ki ce za ki hada da yawa. Duk runtsi kada ya wuce guda uku. Idan kina ga kamar ukun ma zai ba ki wahala ki harhada guda biyu kacal. A hankali hannunki yana gogewa za ki dinga karawa. Har za a kai lokacin da za ki fara hada guda takwas ma.
10- ki tabbata a non stick pan ne, ko kuma wanda kika san ba ya kamawa. Don idan ya kama dukkansu za su lalace ne.
Akwai kayatattun kayan kitchen a Bakandamiya Shopping. Suna da original non stick pan wanda za ki yi aikin samosa da shi.