Skip to content

Yadda ake red velvet doughnut

red velvet doughnut images 1
0
(0)

Da yawa sun dauka cake ne kawai ake yin red velvet dinsa, wasu kuma sun san ana yi amma recipe dinsa bai zo wajajenmu ba sai dai a kasashen ketare. To albishirinku! Nesa ta zo kusa. A yau na kawo maku yadda ake yin haddadden wannan milky red velvet doughnut din tare da vanilla and chocolate filling dinsa.

Abubuwan bukata:

1- 2 cups flour

2- 1/4 cup sugar

3- 1/2 egg

4- 1 tablespoon cocoa powder

5- 1/2 cup buttermilk

6- 2 tablespoons blue band

7- 1/2 teaspoon red velvet powder

8- pinch of salt

9- 1 cup powdered milk

For the filling:

1- 1 cup powdered milk

2- 1/2 cup condensed milk

3- 2 sachets cowbell chocolate milk

Yadda ake yi:

1- ki zuba buttermilk a cikin mixing bowl. Ki zubar sugar, egg, da flour.

red velvet doughnut 2

2- sai ki sa cocoa powder, salt, red velvet powder, da blue band. Ki kai a mixer ta buga miki shi na tsawon minti goma zuwa sha biyar. Idan kuma babu mixer to ki buga da hannu na tsawon minti talatin.

red velvet doughnut 3

3-  ga shi nan bayan na gama bugawa. Sai ki datsa shi daidai girman da kike so sannan ki yi moulding dinsa ki tabbatar ko’ina ya rufe yadda ba zai iya budewa ba.

red velvet doughnut 4

4- Daga nan sai ki bari ya tashi na minti arba’in zuwa awa daya. Sai ki dora mai amma kada ki bari ya yi zafi sosai, kuma kada ki cika wuta da yawa. Sai ki saka doughnut dinki ki soya.

red velvet doughnut 5

5- ki samu kyakkyawna bowl, ki zuba madarar gari da condense milk, ki motse su hade. amma kada ki juye madarar garin za ki rage kadan. Sai ki raba shi biyu. Na farkon ki zuba chocolate din nan a ciki.

red velvet doughnut 6

6- Shi kuma na biyun za ki karasa juye wannan madarar da kika rage ne. Sai ki samu piping bag ki zuba kowanne a ciki.

red velvet doughnut 7

7- ki saka a fridge na minti biyar zuwa goma saboda ya kama jikinsa da kyau kada kina zubawa yana zurara.

red velvet doughnut 8

8- sai ki dauki doughnut ki saka a cikin madarar gari ki tabbatar ko’ina ya samu. Sannan ki bula tsakiyar ki zuba wannan filling da kika hada. Na zuba chocolate chips a sama amma ba dole ba ne.

red velvet doughnut 9

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×