Skip to content

Yadda ake red velvet cake

Share |
Yadda ake red velvet cake
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Mu koyi yadda ake red velvet cake cikin sauki, abubuwan hadawa guda takwas, matakai guda biyar.

Abubuwan hadawa

  1. Flour 2cups
  2. Madara ta gari kofi 1 sai a dama da ruwa kofi 1 sannan a matsa lemon tsami rabi a ciki.
  3. A narkar da butter rabin kofi
  4. Sugar rabin kofi
  5. Baking powder cokali biyu
  6. Kwai guda biyu
  7. Coco powder (poda ce baqa me kalan bonbita) rabin kofi
  8. Jan kala (zaki yi ta zubawa har sai kin ga yayi jazur)

Yadda ake hadawa

  1. Za ki hade duka abubuwan da na lissafa a sama ki cakude su wuri guda ki tabbatar sun hade sossai kaman yadda za ki gani a hotonnan!
  2. Yana hadewa za ki samu abin gashin cake ki shafe sa tas da butter sannan sai ki zo ki zuba kwabin red velvet cake dinki a ciki ki saka a oven ki gasa na kimanin minti shabiyar a wuta madaidaici!
  3. Ki rika dubawa har sai  ya yi, ta yadda za ki gane ya yi shine ki sami tsinken tsokaci (tooth pick) ki tsikara a ciki ki ciro, inkinga ya fito tsaf ba tare da qullin cake a jikinsa ba to cake dinki ya yi!
  4. Abu na gaba shine za ki sami garin whipping cream (ana saidawa a kasuwa)
    Ki dibi kofi daya sai ki zuba masa madara mai sanyi kalau rabin kofi, in kina da mixer ki yi ta bugawa da shi in babu ki yi ta bugawa da hannunki za ki ga ya yi kauri ya yi fari tas, bayan cake dinki ya huce sai ki bi ki shafe shi tas da whipping cream dinki da ki ka kada ya yi kauri!
  5. Za ki iya yiwa cake dinki kwalliya ta diban burbudin cake din na ki ki watsa a samanshi!
    Zai bada armashi matuka, bai da wahalar yi!

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×