Skip to content

Yadda ake rainbow steamed cake

Share |
yadda ake steamed rainbow cake
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake rainbow steamed cake mai dadi da kuma kayatarwa. Ga recipe din a zayyane step by step domin jin dadin bi.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi 1
  2. Kwai 4
  3. Man gyada kofi ¼
  4. Madara kofi 3/4 
  5. Baking powder cokali 1 karami (tsp)
  6. Food colour (pink, green, purple)
  7. Sugar kofi ½ 
  8. Vanilla flavour
  9. Gwangwani gashi
  10. Butter
  11. Flour Steamer

Yadda ake hadawa

  • Ki fasa kwai ki raba ruwan farin kwan a wani kwano daban, kwanduwar itama a wani kwano daban.
  • ki sa Kwanduwar a cikin mixer machine tare da sugar cokali 2 (Tbsp), sai ki yi ta mixing na minti 5, sai ki kawo madara flavour ki sa a ciki ki ta juyawa, kawo man gyada ki sa a ciki ki ta juya shi, ajiye a gefe.
  • Dauko filawa ki tankade ki sa gishiri, baking powder sai ki juya su.
  • Sai ki tankade filawa ki sa a cikin hadin Kwanduwar ki ki na zubawa hankali har sai kin gama da filawar.
  • Ki dauko ruwan farin kwan ki sa sugar sai ki ta mixing har sai ya yi fari tass ya yi kauri sosai.
  • Sai ki dauko hadin filawarki ki juye a hankali a cikinsa ki na juyawa a hankali, sai ki raba kullin ki gida 4 ki sa colour a 3 ki bar dayan haka fari.
  • Daura tukunya (steamer) akan wuta ki sa ruwa ya tafaso.
  • Dauko gwangwani gashin bread ki shafa mi shi butter ki barbada filawa a ciki sai ki sa purple colour a farko sai ki daura akan wuta (steamer) ki barshi na minti 5 sai ki dauko ki daura colour na biyu ki sake mayerwa kan wuta haka za ki yi har sai kin gama da kullin ki sauran. Bayan kin gama sawa, sai ki bar shi ya turaru na minti 15-20.
  • Sai ki sauke ki cire a cikin gwangwani ki yanyanka shi sala sala. A ci dadi lafiya.

Mai karatu na iya duba wasu girke girkenmu na baya kamar chocolate cake da yadda ake egg muffin da makamantansu. Sai mun hadu a girki na gaba, ku huta lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake rainbow steamed cake”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×