Ku koyi yadda ake rainbow cake doughnut cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi bakwai da kuma steps bakwai kacal.
Abubuwan hadawa
- Filawa kofi 4
- Kwai 14-15
- Butter 2 (kimar leda 2)
- Baking powder karamin cokali uku (3½ tsp)
- Flavour karamin cokali uku (3 stpn)
- Sugar kofi 2 (ko ki zuba iya zakin da zai mi ki)
- Food colour (blue, green da pink)
Yadda ake hadawa
- Da farko ki tankade filawarki tare da baking powder, sai ki ajiye a gefe. Ki sami mixer machine na ki, ki sa butter ki a cikin wannan kwanon sa (ko ki sami wani kwano daban idan da hand mixer za ki yi) ki yi ta motsa shi nadan wani lokaci.
- Ki kawo sugar ki sa a ciki ki yi ta motsa shi har sai sugar ki ya narke a ciki (wato ba ki jin gudajin sugar a cikin butter).
- Sai ki dauko kwai ki fasa ki yi ta motsa shi (kwan ana so ana sa shine daya bayan daya kuma ana motsa shi bayan kowani sa kwai daya) har ki gama da kwan na ki.
- Ki dauko filawarki da ki ka tankade tare da baking powder (za ki iya raba filawar gida 6) ki na zubawa a hankali a cikin wannan hadin butter har ki gama da flour ki na motsa shi.
- Sai ki dauko kwano guda 4 ki raba kullinki gida uku. Sai ki dauko food colour ki diga a kowani kwano (ko wani kwano kala daban amma kar ki sa colour a daya ). Shi za ki ajiye shi daban (wanda ba a sa colour ba) Ki juya ko wani kwano (kwano 3 ke nan) ajiye a gefe.
- Sai ki dauko abun gashin (shape din abun gashin ya zama shape na abun yin yankan doughnut) Sannan a cikin abun gashin za ki shafa mashi butter a ciki kadan kafin ki zuba kwallin cake din). Daga nan sai ki zuba hadin ko wani kulli blue, pink da green sai fari (agefe daban daban sai ki dan jijjiga container) A hankali (ba a so a cika shi don kar ya zube a lokacin gashi, ki sa su rabi rabi ko ya dan fi rabi don ya yi gashi mai kyau).
- Sai ki sa a cikin magasa (preheated oven) ki gasa, har sai ya gasu (ko idan kinsa tsinke ya fito ba tare da komai a jikinsa ba). Sai ki cire ki bari ya sha iska, sai ki yanyanka shi.
Karin bayani
Idan ba ki da abun gashin za ki iya sa wa a miki a makera da aluminum shape din Kamar na doughnut. A ci dadi lafiya.