Skip to content

Yadda ake potato pie

Share |
Yadda ake potato pie
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Mu koyi yadda ake potato pie cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Uwargida ki gwada ki zo ki bamu labari. Wai sai an gwada…

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi biyu
  2. Butter cokali hudu
  3. Gishiri kadan
  4. Baking powder karamar cokali daya
  5. Dankalin turawa
  6. Maggie
  7. Attarugu
  8. Albasa
  9. Mai
  10. Ruwan sanyi

Yadda ake hadawa

  1. Ki samu roba ki sa filawa, gishiri, baking powder, butter da ruwan sanyi ki kwaba ta sosai sai ki ajiye a gefe.
  2. Ki samu dankalin turawa ki bare ki yanka kanana sannan ki zuba ruwa a tukunya, sai ki zuba ki yi boiling na shi ya nuna, amma kada ki bari ya fara fashewa. In yayi sai ki sauke.
  3. Ki sa mai kadan a pan ki sa dafaffiyar dankalin taki, kisa albasa, attarugu, Maggie, da gishiri kadan ki motsa su sai ki sauke.a
  4. Sai ki dauko filawa da kika kwaba kiyi rolling sai ki yanka round, koda cutter koda murfin kofi.
  5. Sai ki zuba hadin dankalin ki a sakiya, sai ki nade ki danne bakin da fork. haka za ki yiwa sauran ma. Sai ki shafa mai, butter ko ruwan kwai a sama.
  6. Ki kunna oven yadan yi zafi sai ki sa ki gasa.

Karin bayani

  1. Kada ki cika wuta in kinzo gashi.
  2. In bakida ruwan sanyi za ki iya amfani da ruwa haka.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×